Isa ga babban shafi
Amurka-Taliban

Taliban ta kammala cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka

Yanzu haka dai Amurkan ta alkawarta janye dakarun na ta daga Afghanistan cikin watanni 18 masu zuwa don bayar da damar tabbatar da zaman lafiya a kasar
Yanzu haka dai Amurkan ta alkawarta janye dakarun na ta daga Afghanistan cikin watanni 18 masu zuwa don bayar da damar tabbatar da zaman lafiya a kasar Handout / Afghan Presidential Palace / AFP

Jakadun Amurka na musamman da suka kammala tattaunawa da Wakilcin Taliban sun ce sun cimma yarjejeniya tsakaninsu da kungiyar don kawo karshen yakin kasar Afghanistan na shekaru 17.Yarjejeniyar wadda aka kulla a tattaunawar karshe tsakanin Taliban da wakilcin na Amurka a Qatar ta kunshi tsagaita wuta da kuma janye dakarun kasashen ketare daga Kabul.

Talla

Tawagar jakadun na Amurka karkashin jagorancin Zalmay Khalilzad ta ce an samu gagarumar nasara a tattaunawar wadda aka shafe tsawon watanni ana yi tsakaninsu da Taliban wadda ta kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta daga bangarorin gwamnati da na Mayakan baya ga daukar aniyar janye dakarun kasashen ketare daga Afghanistan.

A cewar Khalilzad wanda ya shafe lokaci ya na shawo kan mayakan na Taliban kan su amince da tattaunawar sulhun, kafin yanzu mayakan na zargin mahukuntan Kabul da yunkurin mayar da su karkashin ikonsu, amma a yanzu bayan tattaunawar ranar Lahadi sun gamsu da matakin sai dai ba su kammala amincewa da yarjejeniyar ba har sai zuwa lokacin da za a fitar da jadawalin kwashe jami’an ketare daga kasar.

Ko a ranar Asabar kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya ce baza su sanya hannu ko kuma yin amanna dari bisa dari da yarjejeniyar ba har sai sun ga zahirin fara kwashe sojin na ketare, wanda Amurkan ta alkawarta kwashe su cikin watanni 18.

Bugu da kari jakadan na Amurka Khalilzad ya ce Taliban ta musu alkawarin hada hannu don kalubalantar kungiyar al’qaeda da ta IS don tabbatar da cikakken tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.