Isa ga babban shafi
Saudiya-Pakistan

Saudiya za ta zuba jarin Dala biliyan 20 a Pakistan

Yarima Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan, Imran Khan
Yarima Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan, Imran Khan reuters

Saudiya ta yi alkawarin kulla yarjejeniyar zuba hannayen jari na Dala biliyan 20 da Pakistan wadda ke fafutukar farfado da tattalin arzikinta da ke cikin mummunan hali.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiya, Mohammed bin Salman ya isa kasar ta Pakistan a ziyarar da ya fara gudanarwa a kasashen yankin Asiya watanni biyar bayan dambarwar kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi, da ake zargin Yariman da hannu a ciki.

Kasar Pakistan na fuskantar matsalar kudi, in da rahotanni ke cewa, Dala biliyan 8 ne kacal a cikin asusun ajiyarta na kasar wajen, yayin da take ci gaba da neman tallafin kasashen ketare.

Gwamnatin Pakistan ta ce, za ta karrama Yarima Salman da lambar yabo mafi girma da take bai wa fararen hula da zaran an kammala kulla yarjejeniyar biliyoyin Dalar.

A banagare guda, Saudiyar ta lashi takobin sassauta tashin hankalin da ake fama da shi tsakanin Pakistan da India.

Wannan na zuwa ne bayan India ta ce, za ta mayar da zazzafan martani bayan wani harin-kunar bakin wake da ya kashe dakarunta 41 a yankin Kashmir, yayin da ake ta kiaye-kirayen Indian da ta dauki mataki kan Pakistan biyo bayan wannan farmakin.

Har ila yau, Yariman da ake yi wa lakabi da MBS, ya yi alkawarin sakin dubban Fursunonin Pakistan da ke garkame a gidan yarin Saudiya.

Ana saran Yariman ya kwashe kwanaki biyu a Pakistan kafin ya wuce India da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.