Isa ga babban shafi
Asiya

Zaben hukumar kwallon kafar Asiya

Sarkin Bahrein tareda rakiyar Yarima Salmane
Sarkin Bahrein tareda rakiyar Yarima Salmane REUTERS/Hamad I Mohammed

A zaben Shugaban hukumar kwallon kafar yankin Asiya,wasu daga cikin yan takara da suka hada da Saoud Al Mohannadi,Mohamed Khalfan Al Romathi sun sanar da janye takarar su don baiwa Sheikh Salman Bin Ibrahim Al Khalifa damar lashe zaben da za a yi farkon watan Afrilun shekarar bana.  

Talla

Wasu daga cikin hukumomin dake da nauyin tafiyar da kwallon kafa a yankin da suka hada da Hukumar QFA ta Qatar ta bayyana goyan bayan ta zuwa dan takara a kujerar Shugabancin hukumar kwallon kafar yankin Asiya Sheikh Salman Bin Ibrahim Al Khalifa.

Dan takara Sheikh Al Khalifa da ya gana da Mohamed Khalfan Al Romaithi ya bayyana farin cikin sa da kuma tabbatar da kawo sauyin da ya dace a wannan tafiya.

Sheikh Al Khalifa na daga cikin masu takar gaggarumar rawa wajen tafiyar da harakokin kwallon kafa a yankin.

A watan Afrilun shekarar 2019 ne ake sa ran zaben sabon Shugaban hukumar kwallon kafar yankin Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.