Isa ga babban shafi
Asiya

Iran ta yi gargadi kan yadda kasashe ke kokarin wargaza tsaro kan ruwa

Hassan Rohani Shugaban kasar Iran a lokacin da yake jawabin sa dangane da halin da yankin yake ciki
Hassan Rohani Shugaban kasar Iran a lokacin da yake jawabin sa dangane da halin da yankin yake ciki HO / Iranian Presidency / AFP

Kasar Saudiya ta ce, an lalata mata tankokin mai guda biyu a wasu hare-hare da aka kaddamar da gangan a yankin tekun Persia, inda ake samun takun-saka tsakanin Amurka da Iran.Yanzu haka sakataren harakokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya soke ziyarsa zuwa birnin Moscow , ya canza balaguron sa zuwa Brussels domin tattaunawa da hukumomin kungiyar Tarayyar Turai kan batun Iran.

Talla

Gwamnatin Iran ta bukaci gudanar da bincike kan hare-haren na yankin Gulf, yayinda ta yi gargadi kan yadda kasashen ketare ke kokarin wargaza tsaron kan ruwa a yankin.

Haka zalika kasar Birtaniya ta bayar da gargadi game da tashin hankalin da ka iya barkewa a yankin.

Tuni dai Amurka ta karfafa dakarun sojinta a yankin na tekun Gulf, inda kuma ta girke jiragen sama masu ruwan bama-bamai samfurin B-52 a matsayin martani ga barazanar da aka ce tana kunno kai daga Iran.

Wasu labarai dake kuno kai daga yankin, Saudiya da ta kasance babbar mai hamayya da Iran, ta soki hare-haren gangancin da ake ci gaba da kai wa jiragen ruwan fareren hula da na ‘yan kasuwa a kusa da gabar ruwan Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ko a jiya Lahadi, sai dai Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce, an kai farmaki kan jiragen ruwa na wasu kasashe daban daban a gabar ruwan masarautar Fujairah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.