Isa ga babban shafi
India-Zabe

Hukumar zaben India ta fara kirgen kuri'un zaben kasar

印度举行第17届国会下院大选第一阶段投票。
印度举行第17届国会下院大选第一阶段投票。 路透社。

Hukumar Zabe a India ta fara kidaya kuri’un zaben 'yan Majalisun da aka gudanar, inda masu kada kuri’a kusan miliyan 600 suka zabi Yan takarar su, daga cikin mutane miliyan 900 dake da rajista.

Talla

Sakamakon farko na nuna cewar, Jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ke kan gaba wajen samun nasara, amma 'yan adawa na fatar samun Karin kujeru.

Jam’iyyun siyasa sama da 1,400 suka shiga zaben yan Majalisun a Majalisar kasar mai wakilai 545.

Zaben dai shi ne mafi girma a tarihin duniya ta fuskar yawan jama'ar da suka kada kuri'a da kuma tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da zaben.

Kafin yanzu dai wasu hasashe na nuna cewa abu ne mai wuya Jam'iyyar Firaminista Narendra Modi ta samu gagarumar nasarar da ta saba samu dai lokacin da ta fuskanci baraka a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.