Isa ga babban shafi
Iran-AMurka

Iran za ta bijire wa yarjejeniyar nukiliya

Shugaban Iran, Hassan Rohani
Shugaban Iran, Hassan Rohani Official President website/Handout via REUTERS

Iran ta ce za ta ninka aikin samarwa, tare da tace makamashin nukiliyarta da take tarawa, har sai ta zarce iyakar da aka mata karkashin yarjejeniyar da ta kulla da manyan kasashen Turai, lamarin da ya zafafa matsin lamba kan batun, tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar a shekarar da ta gabata.

Talla

A ranar 8 ga watan Mayu, shugaba Hassan Rouhani ya bada sanarwar cewa Iran zata daina yin biyayya da ka’idojin da aka shimfida mata kan makaman nukiliyarta, a karkashin yarjejeniyar shekarar 2015.

Ya ce wannan mataki martani ne ga yin gaban – kai da Amurka ta yi na janyewa daga yarjejeniyar tun ba a kai ko ina ba, sannan ta kakaba mata takunkuman karayar tattalin arziki.

Tun daga lokacin aka shiga zaman dar dar tsakanin Iran da Amurka, inda Amurkan ke ta kara yawan dakarunta a yankin Gabas ta Tsakiya, sannan ta kuma sanya dakarun tsaron Iran na musammam a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Iran dai ta yi barazanar ci gaba da kin yin biyayya da yarjejeniyar daga 8 ga watan Yuli, har sai sauran kasashen da ke cikinta, wato Birtaniya, China, Faransa, Jamus da Rasha sun nemi hanyar da za su taimaka mata wajen samun sa’ida, game da takunkuman da aka kakaba mata, ta inda za ta samu ta rika sayar da man ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.