Isa ga babban shafi
Iran-AMurka

Iran ta kakkabo jirgin Amurka marar matuki

Dakarun kare juyin - juye - hali na Iran
Dakarun kare juyin - juye - hali na Iran STRINGER / afp

Sojoji kare juyin juya halin kasar Iran sun sanar da harbo wani jirgin leken asiri maras matuki mallakin Amurka wadanda a cewarsu yana kokarin ratsa sararin samaniyar kasar.

Talla

Tashar talabijin ta Press TV mallakin kasar ta Iran, ta ce ce jirgin, samfurin Global Hawk, an harbo shi ne a yankin Hormozgan da ke kudancin kasar.

Lamarin dai na faruwa ne a wani yanayi da ake kara zaman tankiya tsakiya Iran, Amurka da kuma wasu kasashen Larabawa musamman Saudiyya.

Ana ci gaba da kallon hadarin kaji tsakann Amurka da Iran, tun da shugaba Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar 2015 a watan Mayun shekarar da ta gabata.

Dimbim takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran sun yi mumunan tasiri a tattalin arzikinta, wadda dama can yake gamuwa da cikas.

Amurka ta kara wa dakarunta da ke yankin Gabas Ta Tsakiya damara, a wani kokari na karfafa matsin lamba ga Iran, lamarin da ya sa ake fargabar cewa wani yaki na daf da barkewa a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.