Isa ga babban shafi
Duniya

Amurka ta sanya kungiyar yantar da Baluchistan cikin kungiyoyin yan ta’adda

Mayakan kungiyar Baluchistan
Mayakan kungiyar Baluchistan AFP PHOTO/FARSNEWS/STR

Kasar Amurka ta bayyana kungiyar dake fafutukar yancin Baluchsitan dake kasar Pakistan a matsaytin kungiyar yan ta’adda bayan ta kai hari kan muradun kasar China.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewar ta sanya kungiyar yantar da Baluchistan cikin kungiyoyin yan ta’adda na duniya ne saboda hare haren da take kaiwa jami’an tsaro da kuma fararen hula.

A karkashin wannan shiri, yanzu ya zama laifi ga duk wani mutum ko wata hukuma ko kuma kasa tayi hulda da ya’an kungiyar, yayin da Amurka zata rufe duk wani asusun ajiyar kudade dake da nasaba da kungiyar a kasar ta.

Rahotanni sun ce kungiyar ta Baluchsitan ta dade tana kai munanan hare hare kan yan kasar China dake Pakistan, ciki harda ofishin jakadancin China dake Karachi, inda suka kashe mutane 4 a watan Nuwamba.

A watan Mayu, mutane 5 suka mutu sakamakon harin kungiyar a wani otel, cikin su harda soji guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.