Isa ga babban shafi
Hong Kong

'Yan sandan Hong Kong sun sake arangama da masu zanga-zanga

Wasu masu zanga-zanga a Hong Kong
Wasu masu zanga-zanga a Hong Kong REUTERS/Edgar Su

Jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye kan dandazon masu zanga-zanga a Hong Kong matakin da ke zuwa bayan zargin da gwamnati ta yin a cewa ‘yan sanda na kin daukar matakin kwantar da tarzomar yankin.

Talla

Dubun-dubatar mutane ne dai, suka rufe fuskokinsu tare da yin dandazon da nufin sake rufarwa Ofishin China da ke arewacin yankin Yuen Long kamar yadda suka yi a makon jiya.

Mako na 7 kenan Hong Kong na fuskantar kazamar zanga-zangar boren ga gwamnati tun bayan kudirin da ya nemi fara aikewa da masu laifi China don fuskantar hukunci, mayakin da ya ci karo da kundin tsarin mulkin da ma yarjejeniyar mika yanking a China da aka cimma da Birtaniya.

Duk da cewa gwamnati ta janye kudirin dokar, yanu haka masu zanga-zangar na neman murabus din shugabar yankin tare da bin kadion hakkokin wadanda jami’an tsaro suka ciwa zarafi yayin zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.