Isa ga babban shafi
Yemen

Adadin mutanen da suka halaka a hare-haren Yemen ya karu

Bangaren sansanin jami'an tsaron Yemen na Al-Jala dake yammacin birnin Aden da 'yan tawayen Houthi suka kaiwa farmaki.
Bangaren sansanin jami'an tsaron Yemen na Al-Jala dake yammacin birnin Aden da 'yan tawayen Houthi suka kaiwa farmaki. AFP / Nabil HASAN

Hukumomin Kasar Yemen sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da mayakan Houthi suka dauki alhakin kaiwa a birnin Aden ya kai 49, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Talla

Hare-haren su ne na farko a garin dake dauke da tashar jiragen ruwa, a cikin shekara guda, matakin dake nuna gazawar matakan tsaron da gwamnatin kasar ke dauka.

Mohammed Rabid, babban jami’in ma’aikatar lafiya, yace bayan mutane 49 da suka mutu, wasu 48 sun jikkata.

Mai magana da yawun kungiyar Yan Tawayen Houthi ya bayyana cewar sun kai harin ne da wani makamin da basu saba amfani da shi ba, da kuma jirgi mai sarrafa kan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.