Isa ga babban shafi
Hong Kong

Zanga-zanga ta nakasa tattalin arzikin Hong Kong

Masu zanga-zangar na arangama da jami'an 'yan sand a duk rana ta Allah
Masu zanga-zangar na arangama da jami'an 'yan sand a duk rana ta Allah Reuters

Shugabar Gwamnatin Honk Kong, Carrie Lam ta gargadi cewa, zanga-zanga rajin mulkin dimokradiya da aka kwashe watanni biyu ana gudanarwa, na haifar da gagarumar illa ga tattalin arzikin yankin, yayinda ta bayyana shirinta na cimma matsayar kawo karshen boren.

Talla

Shugabar Gwamnatin Hong Kong da ke cikin tsaka mai wuya ta gana da jagororin ‘yan kasuwa a daidai lokacin da dubban al’ummar yankin ke zaman dirshen a filin jiragen sama, inda suke fatan samun goyon bayan kasashen duniya game da zanga-zangarsu ta rajin mulkin dimokradiya.

Sai dai shugaba Carrie Lam ta gargadi cewa, Hong Kong na fuskantar mummunar barazar tabarbarewar tattalin arziki da ta zarce wadda aka gani a shekarar 2003 da kuma shekarar 2008.

Lam ta ce, za a dauki dogon lokaci kafin yankin ya gyagije daga matsalar tattalin arziki.

Tuni dai kamfanoni masu zaman kansu da suka hada da kamfanonin kula da masu yawan bude ido, suka bayyana damuwa kan illar da zanga-zangar ke yi wa tattalin arzikin yankin, yayinda hukumomi ke cewa, an samu raguwar masu shige da fice da kashi 50 cikin 100 a yankin.

Zanga-zangar dai ta samo asali ne saboda shirin gwamnatin yankin na tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskntar hukunci,  kuam har yanzu jama’a na ci gaba da boren a duk rana ta Allah tare da arangama da jami’an ‘yan sanda, abinda ya sa kasashen duniya da dama suka hana al’umominu balaguro zuwa yankin a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.