Isa ga babban shafi
Asiya

Tsokacin kasashen Duniya dangane da rikicin Hong Kong

Motocin tarwartsa masu zanga-zanga  a Hong Kong
Motocin tarwartsa masu zanga-zanga a Hong Kong REUTERS

Kungiyar Tarayar Turai ta bayyana rashin amincewa da kame da Hukumomin Hong Kong ke yiwa masu rajin kare demokradiya, yayinda mahukuntan China ke cewa sam babu zancen lallashin masu bore da ake yi.

Talla

Irin abubuwan dake aukuwa a HongKong dan tsakanin nan babu dadi ji ko kadan, kalaman

Uwargida Federica Mogherini mai Magana da yawun kungiyar Turai .

Tana mai bukatar ganin mahunta a Hong Kong na mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, da ‘yancin gudanar da taro.

A yau Juma’a dai mahukunta a Hong Kong din suka farma masu rahin kare demokradiya ciki har da wakilin majalisa saboda bore da suke yi, al’amarin da suke cewa kasar China ke ingiza wannan kamen da niyar rufe bakin masu boren.

Matakin kamen na zuwa ne gabanin wani gagarumin zanga-zanga da kungiyoyi suka shirya yi gobe Asabar, wanda kuma rundunar ‘yan sandan Hong Kong ke sanar da haramtawa.

Watanni 3 kenan dai ake ta wannan bore a yankin na Hong Kong, inda ake samun mummunar karawa tsakanin ‘yan sanda da masu boren.

Ita dai kasar China dake cewa yankin nata ne, ta hau kujeran naki, game da matakan lallashin masu bore da mahukuntan yankin ke yi.

Hukumomin Hong Kong sun saar da sako wasu daga cikin masu boren a yau juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.