Isa ga babban shafi

India ta saki mayakan Taliban don musayar Injiniyoyinta 7

Wasu jagororin kungiyar Taliban
Wasu jagororin kungiyar Taliban KARIM JAAFAR / AFP

Wata majiya daga Afghanistan ta bayyana cewa India ta amince da sakim wasu manyan kwamandojin Taliban 11 don musayar injiniyoyinta 7 da kungiyar ke tsare da su.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa tuni Taliban a na ta bangaren ta saki Injiniyoyin 7  wadanda ta ke tsaro da su fiye da shekara guda, bayan matakin damka mata mayakan na ta.

Matakin na zuwa ne dai dai lokacin da a karon farko Taliban ta sanar da ganawa da jakadan Amurka kan tattaunawarsu Zalmay Khalilzad tun bayan matakin Amurka na janyewa daga tattaunawar bayan kisan Sojinta guda.

Haka zalika nasarar ta Taliban kan India wajen ganin an sakar mata manyan mayakan har 11 na zuwa a dai dai lokacin da ake cika shekaru 18 cif da fara yakin kasar da Amurka ta kaddamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.