Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Kasashen Duniya na kira zuwa Shugaban Turkiya

Mutanen yankunan kurdawa a Syria na tserewa daga yankunan su
Mutanen yankunan kurdawa a Syria na tserewa daga yankunan su Delil SOULEIMAN / AFP

Farmakin da Turkiya ta kaddamar a Syria na ci gaba da jan hakulan manyan kasashen Duniya dake ci gaba da yi kira zuwa Shugaban Turkiya Recep Tayib Erdogan da ya kawo karshen wannan yaki.

Talla

A jiya juma’a Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Amurka Donald Trump ,ya bukaci ganin Amurka ta taka gaggarumar rawa don kawo karshen wannan yukunrin Turkiya.

Shugaba Macron ya bayyana cewa Faransa da Amurka za su hada gwuiwa don samar da wani tsarin da zai taimaka na kawo karshen hare-haren da Turkiya ke kaiwa zuwa yankunan kurdawa dake Syria.

Yunkurin Turkiya ya tilastawa kusan mutane dubu 60 tserewa daga wadanan yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.