Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya-Jamus

Turkiya ta bijirewa bukatar janye farmaki kan Kurdawa a Syria

Wasu daga cikin dakarun kawancen rundunar da sojojin Turkiya ke jagoranta, yayin da suka kutsa yankin arewacin Syria. 11/10/2019.
Wasu daga cikin dakarun kawancen rundunar da sojojin Turkiya ke jagoranta, yayin da suka kutsa yankin arewacin Syria. 11/10/2019. exodus. Nazeer Al-khatib/ AFP

Dakarun Turkiya sun kara azamar farmakin da suka kaddamar kan mayakan Kurdawa masu iko da wasu garuruwa a arewacin Syria, dake kan iyakar kasashen biyu.

Talla

Ma’aikatar tsaron Turkiya, ta ce dakarun kasar sun yi nasarar kame birnin Ras al-Ain, yanki na farko da suka kwace daga hannun mayakan Kurdawan.

Dakarun na Turkiya na ci gaba da azamar ce, duk da barazanar daukar matakan kakabawa kasar takunkumi da wasu kasashe ke yi ciki har da Amurka.

Zuwa yanzu fararen hula sama da dubu 100, suka tsere daga muhallansu, bayan kaddamar da hare-haren da Turkiya ta yi kan Kurdawan a Syria.

A baya bayan nan Jamus ta sanar da shirin haramta cinikin makamai tsakaninta da Turkiya, sakamakon farmakin da dakarun kasar ke ci gaba da kaiwa kan mayakan Kurdawa YPG a arewacin Syria, lamarin daya jefa dubban fararen hula cikin tashin hankali, da kuma bijirewa kiraye-kiyaren dakatar da hare-haren da Turkiyan ta yi.

Jamus na daga cikin kasashen dake kan gaba wajen kera makamai da saida su a duniya, baya ga Amurka, China, Rasha, Birtaniya da kuma Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.