Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta janye dakarunta dubu 1 daga arewacin Syria

Wasu sojin Amurka a gaf da motar dakarun Turkiya a arewacin Syria. 8 ga Satumba, 2019.
Wasu sojin Amurka a gaf da motar dakarun Turkiya a arewacin Syria. 8 ga Satumba, 2019. AFP/Delil Souleiman

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon, ta bada umarnin janye dakarun kasar dubu 1, daga arewacin kasar ta Syria, a dai dai lokacin da ake musayar zafafan kalamai tsakanin Turkiya da kasashen Faransa da Jamus kan hare-haren da ta kaddamar kan Kurdawa a Syria.

Talla

Matakin bazatar janye dakarun Amurkar ya zo ne, a dai dai lokacin da adadin fararen hular da suka tagayyara, sakamakon hare-haren Turkiyan a Syria ya zarta dubu 130.

A baya bayan nan Faransa ta bayyana kaduwa kan barin wutar da dakarun Turkiya ke ci gaba da yi a arewacin Syria, bayan da Kurdawan suka ce kimanin ‘yan uwan mayakan IS 800 sun samu damar tserewa sakamakon rushewar gidan Yarin da suke ciki a dalilin farmakin na Turkiya.

Ranar asabar Faransa da Jamus suka yanke alakar saidawa Turkiya makamai, saboda watsin da ta yi da kiraye-kirayen dakatar da hare-haren da ta kaddamar a arewacin Syria da zummar murkushe mayakan Kurdawan YPG.

Sai dai shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan yace takunkumin haramtawa kasar sayan makamai da kasashen Faransa da Jamus suka kakaba mata, ba zai dakatar da aniyarsu ta murkushe mayakan Kurdawan YPG, da suke kallo a matsayin ‘yan ta’adda ba.

Turkiya dai ta dade tana hankoron afkawa mayakan na YPG dake arewacin Syria, wadanda take kallo a matsayin reshen haramtacciyar jam’iyyar Kurdawa ta PKK, wadda a shekaru baya ta shiga yakin neman ballewar kasar Kurdawa daga cikin Turkiya.

To sai dai mayakan Kurdawan sun kasance kawayen kasashen Turai da Amurka, wadanda suka taka muhimmiyar rawa cikin rundunar kawancen da ke yakar kungiyar IS a Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.