Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin bam ya halaka mutane 62 a Masallaci

Jami'an agaji yayin kokarin fitar dawani mutum da harin bam ya ritsa da shi a Masallacin Juma'ar lardin Nangahar dake Afghanistan.
Jami'an agaji yayin kokarin fitar dawani mutum da harin bam ya ritsa da shi a Masallacin Juma'ar lardin Nangahar dake Afghanistan. NOORULLAH SHIRZADA / AFP

Wani harin bam yayi sanadin salwantar rayukan fararen hula 62, tare da jikkata wasu 36, yayinda suke halartar Sallar Juma’a a lardin Nangahar.

Talla

Hukumomin kasar ta Afghanistan dai sun bada bayanai mabanbanta kan tushen harin, inda gwamnan lardin na Nangahar Ataullah Khogyani ya ce an dasa bama bamai 2 ne cikin masallacin Juma’ar.

Sai dai kakakin shugaban kasar Sadiqi Saddiqi ya ce wani dan kunar bakin wake ne ya tarwatsa kansa a Masallacin.

zuwa lokacin da muka wallafa wannan labarin dai, babu wata kungiya, da ta dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar mayakan Taliban, tayi Allah-wadai da harin, tare da bayyana shi a matsayin ta’addancin kungiyar IS, ko kuma gwamnatin kasarta Afghanistan.

Wani rahoton majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis, ya ce hare-haren bam kan wuraren da fararen hula ke taruwa yayi sanadin halakar adadin da ya kai 647 da kuma jikkata wasu dubu 2 da 796, daga watan Janairun 2019 zuwa Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.