Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Erdogan ya ce: "zan darkake Mayakan kurdawa idan ba su ficedaga gabashin Syria ba nandaranar talata.

shugaban Turkiya, Recep Erdogan
shugaban Turkiya, Recep Erdogan Kayhan Ozer/Presidential Press Office/Handout via REUTERS

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar darkake mayakan kurdawa da ke yankin arewa maso gabashin kasar Syriya, idan basu janye daga yankin ba, har wa’adin da aka basu zuwa ranar talarta ya cika.

Talla

A cikin wani ja’awabi da ya gabatar a garin Kayseri, dake cikin yankin Anatolie Shugaba Edogan yace da zarar wa’adin awowi 120 da aka bawa kurdawan kan su fice daga yankin ya cika, to kuwa dakarun Turkiya a za su da zabi face ci gaba ne daga iyar da aikin da suka dakatar na darkake dakarun Kurdawan da ya kirada yan ta’adda.

Sai dai a na sa bangaren, shugaban kungiyar dkarun tabbatar da demokradiya a Syriya, (FDS), da ta hada mayakan kudawa da larabawa, da kuma ke kawance da rundunar dakarun kasashen duniya, da ke fada masu ikrarin jihadi karkashin jagorancin Amruka.

Mazloum Abdi ya ce, sun kaddamar da wasu sabin hare-hare kan wasu sansanonin mayakan jihadin kungiyar ISI, a Deir Ezzor, kwanaki 3 bayan da kungiyar ta FDS ta bayyana dakatar da yakin da take yi, da mayakan na Isis sakamakon hare haren da turkiya ke kai wa kan dakarun na Kurdawa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.