Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta karkata akalar dakarunta zuwa gadin rijiyoyin mai

Wasu motocin sojin Amurka yayin tsallakawa cikin Iraqi, bayan janyewa daga arewacin Syria.
Wasu motocin sojin Amurka yayin tsallakawa cikin Iraqi, bayan janyewa daga arewacin Syria. Safin Hamed/AFP/Getty Images

Masana na ci gaba da tafka muhawara kan matakin shugaban Amurka Donald Trump, na karkatar da akalar dakarun kasar da ya janye daga yankin Kurdawa a Arewacin Syria zuwa gadin filayen hakar man fetur a birnin Dier Ezzor, da shi ma ke arewacin kasar ta Syria.

Talla

A wannan Juma’a Sakataren tsaron Amurka Mark Esper ya ce a halin yanzu babban aikin dakarun kasar, shi ne tabbatar da cewa, mayakan IS basu samu damar karbe iko da filayen hakar man ba, da kuma dakile duk wani yunkurinsu na kafa sansanin kai hare-haren ta’addanci a yankin.

Ranar 6 ga watan Oktoba, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janye dakarun kasar dubu 1 daga arewacin Syria, wadanda suka yaki kungiyar IS da taimakon mayakan Kurdawa, matakin da ya baiwa Turkiya damar afka musu da yaki a ranar 9 ga watan na Oktoba, 2019.

Turkiya na kallon mayakan Kurdawan na YPG data afkawa a matsayin ‘yan ta’adda, kuma reshen haramtacciyar Kurdawa ta PKK da a shekarar 1984 ta soma gwagwarmayar ballewa daga Turkiya, don kafa kasar Kurdawa zalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.