Isa ga babban shafi
Iraq

Jami'an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga a Iraqi

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iraqi
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iraqi REUTERS/Thaier Al-Sudani/File Photo

Jami’an tsaron Iraqi sun harba harsasai kan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Bagadaza, sa’oi bayan kashe masu zanga-zanga guda 4 a kofar shiga ofishin Jakadancin Iran da ke Karbala.

Talla

Wannan arangama na daga cikin tashin hankali na baya-bayan nan da aka gani a Iraqi, a ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ta kai ga datse hanyoyi da kuma bijire wa gwamnati saboda zargin cin hanci da rashin ayyukan yi.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi ruwan duwatsu kan jami’an tsaro, yayin da jami’an suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashan roba.

Akalla mutane 20 aka jikkata a Bagadaza, kamar yadda hukumomin asibiti suka tabbatar, yayin da 4 suka riga mu gidan gaskiya a Karbala.

Alkaluma sun bayyana cewar, mutane 270 suka rasa rayukansu tun bayan barkewar zanga-zangar a ranar 24 ga watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.