Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta kame masu hannu a kakkabo jirgin Ukraine

Sassan jirgin Ukraine da Iran ta kakkabo bisa kuskure.
Sassan jirgin Ukraine da Iran ta kakkabo bisa kuskure. © Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

Dai dai lokacin da aka shiga kwana na 3 Iran na fuskantar zazzafar zanga-zangar bukatar daukar mataki kan wadanda ke da hannu a kakkabo jirgin Ukraine da ya hallaka ilahirin fasinjan cikinsa mutum 176, a yau Talata gwamnatin kasar ta sanar da kame wasu da ke da hannu a aika-aikar.

Talla

Cikin makon jiya ne, makaman Iran masu linzami suka kakkabo jirgin na Ukraine kirar Boeing 737 mintuna kalilan bayan tashinsa daga filin jirgin saman birnin Tehran dauke da fasinja 176 da sauran jami’an jirgin, batun da a karon farko kasashen duniya suka zargi Iran da aikatawa amma ta musanta.

Sai dai bayan gudanar da jerin binciken Iran ta amsa laifin kakkabo jirgin bisa kuskure yayinda ta gayyaci kasashen duniya kan su gudanar da bincike gano yadda lamarin ya wakana.

Cikin wani sako ta gidan Talabijin da kakakin bangaren shari’ar kasar Gholamhossein Esmaili ya gabatar ya bayyana cewa an kame wadanda ke da hannu a aika-aikar kuma za a zartas musu da hukunci, ko da dai bai fayyace adadin mutanen da aka kamen ba.

Kamen na yau Talata na zuwa ne kasa da sa’a guda bayan sanarwa shugaba Hassan Rouhani da ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a aika-aikar cikin gaggawa.

Cikin kalaman na Rouhani, ya nanata cewa hakki ne akansu su hukunta wadanda suke da hannu a sakacin da ya kai ga asarar rayukan jama’a 176.

A cewar Rouhani za su kafa kotu ta musamman da kwararu ta bangaren shari’a a gaban idon duniya, a gudanar da shari’a tare da zartas da hukunci kan wadanda ke da laifi cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.