Isa ga babban shafi
China-Corona

Wasu kasashe za su kwashe jama'arsu daga China saboda Corona

Wasu da ke kokarin tserewa daga yankin Wuhan na China bayan ta'azzarar annobar cutar Corona da aka fi sani da murar mashako.
Wasu da ke kokarin tserewa daga yankin Wuhan na China bayan ta'azzarar annobar cutar Corona da aka fi sani da murar mashako. 路透社REUTERS/Tyrone Siu

Wasu Kasashen duniya cikin su har da Amurka na shirin kwashe al'ummominsu daga China saboda yadda cutar coronavirus yanzu haka ta hallaka mutane 106 yayinda tuni ta watsu a wasu kasashe ciki har da wadanda ba su ziyarci kasar ta China ba.

Talla

Matakin kasashen na zuwa a dai dai lokacin da shugaban kasar ta China Xi Jinping ke bayyana yadda kasar ta himmatu wajen yaki da cutar ta Coronavirus tare da shan alwashin bayyanawa duniya halin da ake ciki ba tare da kunbiya-kunbiya ba.

A cewar shugaba Xi yayin ganawarsa da shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bayyana cutar da annoba wadda bai kamata kasar ta boye komi game da ita ba.

A bangare guda tuni, WHO ta bayyana cewa babu bukatar kwashe mutanen daga China bisa kaffa hujja da matakan da ake dauka wajen yaki da cutar cikin gaggawa.

Cikin yankin Wuhan mai yawan jama’a fiye da miliyan 7 akwai tarin ‘yan kasashen ketare da ke ciki wanda yanzu haka gwamnatin kasar ta sanyawa dokar ta baci don hana su zirga-zirga da nufin dakile yaduwar cutar, matakin da sanya kasashen fara tunanin kwashe jama’arsu.

Cikin kasashen akwai Japan wadda ke da yawan jama’a 650 ko da dai itama tuni ta sanar da bullar cutar sai Australia mai yawan jama’a 400 kana India wadda ta ce tuni ta shirya jirgin da zai kwaso mutanenta 250 da ke Chinan.

Sauran kasashen sun hadar da Indonesia mai yawan jama’a 234 tukuna Sri Lanka da ke da al’ummarta 860 tukuna Korea ta kudu wadda ba ta bayyana adadin al’ummartata ba, amma ta bayyana shirin kwashe su.

Haka zalika akwai kasashen Thailand maimutane 64 kana Philippines da mutane 150 tukuna Amurka da mutane 250 sannan Faransa wadda itama babu alkaluman al’ummartata a China sai dais ha alwashin kwashesu gabaninkarshen mako.

Cikin kasashen da ke shirin kwashe jama’ar ta su daga China akwai kuma Jamus mai mutane 90 kana Morocco da al’ummarta 100 sannan Spain ko da dai itama babu cikakkun alkaluman al’ummartata a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.