Isa ga babban shafi
India-Pakistan

India ta yi ikirarin iya murkushe Pakistan a kwana 10

Firaministan India Narendra Modi.
Firaministan India Narendra Modi. PRAKASH SINGH / AFP

Firaministan India Narendra Modi ya ce su na da karfin iya murkushe Pakistan cikin kwanaki 10 muddin yaki ya barke tsakanin kasashen biyu da ke makwaftaka da juna.

Talla

Yayin da ya ke jawabi ga sojojin kasar, Modi ya ce sau 3 Pakistan ke shan kashi a hannun India, saboda haka ba zai dauki sojojin su kwanaki 7 zuwa 10 ba wajen murkushe kasar.

A nata martani, Pakistan ta bayyana kalaman Firaminista Modi a matsayin rashin hankali daga mai bukatar yaki.

Tarihi ya nuna cewar kasashen India da Pakistan sun gwabza yaki sau 3 a shekarar 1947 da 1965 da 1971, bayan tashin hankalin da suka samu a tsakanin su a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.