Isa ga babban shafi
China-Birtaniya

Birtaniya ta aike da jirgin kwashe al'ummarta daga China

Jirgin da zai yi aikin jigilar 'yan Birtaniya daga China.
Jirgin da zai yi aikin jigilar 'yan Birtaniya daga China. REUTERS/Hannah McKay/File Photo

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana gobe juma’a a matsayin ranar da za ta fara aikin jigilar al’ummarta daga yankin Wuhan na China bayan tsanantar annobar cutar Coronavirus da aka fi sani da murar mashako a yankin da ya tilasta sanya dokar ta baci baya ga hana shige da fice a yankin.

Talla

A cewar sakataren harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab da sanyin safiyar gobe Juma’a jirgin kasar zai tashi zuwa China don kwaso tarin al’ummarta da suka makale a yankin na Wuhan da China ta sanyawa dokar ta baci.

Matakin acewar ma’aikatar wajen ta Birtaniya na zuwa bayan samun amincewar hakan daga Beijing.

Birtaniya dai na jerin kasashen duniya kusan 30 da ke shirin fara kwashe jama’arsu daga Chinar bayanda adadin mutanen da cutar ta Corono yanzu haka ya karu zuwa 170, yayinda cutar ta watsu zuwa wasu kasashe ciki har da Japan.

Sanarwar da ma’aikatar wajen ta Birtaniya ta fitar ta ce, Ofishin jakadancinta da ke Beijin ya kammala tantance ‘yan kasar da suke yankin na Wuhan kuma tuni ya samu sahalewa daga gwamnatin China game da shirin kwashewar.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis ta mako mai zuwa ko kuma laraba a China ne jirgin dakon ‘yan birtaniyar zai baro yankin na Wuhan bayan kammala binciken kwa-kwaf na lafiya kan mutanen don gudun daukar cutar tare da yadata a Birtaniyar.

Haka zalika wata majiya ta ce ko da bayan kwaso mutanen su fiye da 200 ciki har da ‘yan Spain 50 za kuma su shafe akalla kwanaki 14 a cibiyar gwajin lafiya da ke arewa maso yammacin birnin London don tabbatar da basa dauke da cutar ta Corona da aka fi sani da murar mashako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.