Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Pompeo ya nemi Falasdinawa su kawo shirin da zai gamsar da Isra'ila

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo REUTERS/Erin Scott

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bukaci Falasdinawa da suka yi watsi da shirin shugaban Amurka na sasanta rikicin gabas ta tsakiya, da su gabatar da nasu sabon shirin da zai gamsar da Isra’ila, gami da zabi karbabbe ga kowa.

Talla

Pompeo ya kalubalanci Falasdinawa ne kafin yin tattaki zuwa birnin London, inda a yau zai gana da Fira Minista Boris Johnson kan yadda za su karfafa alaka, bayan ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai a karshen watan nan.

Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya bayyana kwarin gwiwar cewa a shirye Isra’ila take wajen sake tattaunawa da shugabannin Falasdinawa muddin suka gabatar da nasu shirin zaman lafiyar da zai iya zama karbabbe ga kowa.

A ranar Talatar da ta gabata shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da shirinsa da aka dade ana jira kan sasanta rikicin gabas ta tsakiya musamman tsakanin Falasdinawa da Isra’ila, sai dai nan take Falasdinawa suka yi watsi da shirin mai dauke da shafuka 80 da kuma taswirar iyakokin kasashen biyu da ta bayyana cewar Israila zata mallake yankunan Falasdinawa 15 da ta gina gidajen da Yahudawa ke ciki, wadanda ake wa lakabi da Yankunan ‘Yan kama wuri zauna.

Yanzu haka dai kawunan kasashen larabawa da ma na Turai da kuma manyan hukumomi sun rarrabu kan shirin zaman lafiyar, inda wasu ke yabawa, ko kushewa, wasu kuwa zaune suke kan Katanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.