Isa ga babban shafi
China-Corona

Sama da mutane 13,500 sun kamu da Corona, 775 sun mutu

Wani iyaye sanye da mayanin fuska don gudun harbuwa da Corona virus.
Wani iyaye sanye da mayanin fuska don gudun harbuwa da Corona virus. Philip FONG / AFP

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harbuwa da cutar murar mashako ta Coronavirus ya karu zuwa 775 a yau Asabar, abin da ke nuni da cewa ya zarce wadanda cutar SARS ta kashe kusan shekaru 20 da suka gabata.

Talla

Mutane 650 ne suka mutu sakamakon cutar nan mai shafar numfashi SARS a China da Hong Kong daga shekarar 2002 zuwa 2003,kana fiye da 120 suka mutaa sairan sassan duniya.

Karin wasu mutane 86 sun mutu a cewar ma’aikatar lafiya ta kasar China, kuma akasarin su daga yanki Hubei ne, inda aka gano cutar a watan Disamban shekarar da ta gabata.

A bayanin da take kawowa duk rana, ma’aikatar lafiyar ta tabbatar da cewa mutane 3,399 sun harbu da cutar a baya bayan nan, kuma sama da mutane 34,500 sun harbu a fadin kasar.

China tana ta fadi – tashin shawo kan wannan cuta duk data killace mutane akalla miliyan 56 a lardin Hubei da shelkwatar ta Wuhan.

A sauran biranen mahukumomi sun takaita fita, inda mutane na zaune agida don gudunyaduwar wannan cuta.

Mutuwar likitan nan dan shekara 34, wanda shi ya fara gano cutar, ya kuma yi yekuwar gano ta, wanda hakan ya sa hukumomi suka hukunta shi ya janyo tada jijiyoyin wuya kan yadda gwamnati ke tinkarar wannan annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.