Isa ga babban shafi
Asiya

Wani sojin Thailand ya kashe mutane 26

Daya daga cikin sojojin da suka murkushe maharin a cikin kasuwar zamani
Daya daga cikin sojojin da suka murkushe maharin a cikin kasuwar zamani ©REUTERS/Athit Perawongmetha

Rundunar tsaron Thailand ta sanar da kawo karshen garkuwa da mutane da wani soji ya yi da mutane tun a jiya asabar.Sojin dan kasar Thailand da yayi amfani da bindiga ya harbe mutane 26 har layira inda ya kuma raunata da dama a cikin wata kasuwar zamani dake birnin.

Talla

Yan lokuta bayan da sojojin suka yi nasarar kashe maharin ,Firaministan kasar Thailand Prayut Chan-O-Cha ya bayyana alhinin sa,inda ya kuma bayyana maharin da mai fama da wasu matsaloli can daban.

Firaministanm Thailand da ya zarci mutanen da suka samu rauni a asibiti ya bayyana cewa hakan ba zai sake faruwa ba,nan take ya bayar da umurni don ganin an karfafa mataken tsaro a wurin ajiyar makamai dake cikin bariqin sojin da ya kai wannan hari.

Sojin  mai suna Jakrapanth Thomma ya yi awon gaba da wata bindiga mai sarrafa kanta wanda  ya kuma yi amfani da ita  wajen kisan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.