Isa ga babban shafi
Asiya

Yan Rohingya 14 suka nitse a ruwa

Wata mata yar kabilar  rohingya a Bangladesh
Wata mata yar kabilar rohingya a Bangladesh REUTERS/Danish Siddiqui

Akalla yan kabilar Rohingya 14 suka nitse a ruwa yau da safe lokacin da kwale kwalen da suke ciki da yake dauke da mutane da dama ya kife a kudancin kasar Bangladesh.

Talla

Kwamandan dakarun dake kula da gabar ruwa, Naim ul Haq ya sanar da cewar sun ceto mutane 70 da ran su, yayin da suka zakulo gawarwaki 14.

Rahotanni sun ce mutane da dama daga cikin yan kabilar Rohingya sama 700,000 da suka samu mafaka a Bangladesh na kokarin barin kasar zuwa Malaysia ta cikin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.