Isa ga babban shafi
Japan

An karrama mutum mafi yawan shekaru a duniya

Chitetsu Watanabe dattijo dan Japan mafi yawan shekaru a duniya.
Chitetsu Watanabe dattijo dan Japan mafi yawan shekaru a duniya. Reuters

Yau Laraba an karrama sabon mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya daga cikin maza, kuma shi ne Chitetsu Watanabe, mai shekaru 112 a kasar Japan.

Talla

An dai haifi Jitetsu ne a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1907 a Niigata da ke kusa da birnin Tokyo, kuma masu kula da littafin tarihi na ‘Guiness World of Records’ sun tabbatar masa da wannan matsayi na mafi tsufa a duniya daga bangaren maza.

Wanda ya ke rike da matsayin Masazo Nonaka, mai shekaru 112 da kwanaki 266 daga kasar na japan ya rasu a watan jiya.

Watanabe wanda ya ke da mata da yara guda 5, ya bayyana cewar abinda ke tsawaita rayuwar jama’a shi ne rashin yin fushi da fara’a a koda yaushe.

Matar da tafi kowa tsufa a duniya yanzu haka, ita ce Kane Tanaka, yar kasar Japan, mai shekaru 117.

Kasar Japan na da mutanen da suka fi tsufa a duniya saboda yanayin rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.