Isa ga babban shafi
China-Corona

Annobar COVID -19 ta kashe sama da mutane 1350, sama da dubu 60 sun kamu

Wasu ma'aikatan lafiy a China
Wasu ma'aikatan lafiy a China China Daily via REUTERS

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da coronavirus ko kuma COVID-19 ya kai 1,355, yayin da wadanda suka kamu da cutar a kasar china kawai suka zarce 60,000.

Talla

Adadin mutanen da suka mutu daga cutar COVID-19 da kuma sabbin wadanda suka kamu da cutar yayi matukar karuwa bayan da hukumomin kasar suka sauya hanyar da suke kidaya wadanda suka kamu domin kawar da farfagandar da ake yi.

Yankin Hubei da cutar ke ta’addi ta sanar da mutuwar mutane 242 a cikin kwana guda, yayin da sabbin mutane 14,840 suka kamu da cutar, wanda shine mafi yawa tun bayan barkewar annobar.

Wannan adadi ya daga alkaluman da aka samu na wadanda suka mutu zuwa 1,355, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar a China baki daya ya kai kusan 60,000.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya gudanar da wani taron gaggawa kan lamarin, yayin da aka kori shugaban siyasar Yankin Hubei Jiang Chaoling aka kuma maye gurbin sa da Magajin Garin Shanghai Ying Yong, kwana guda bayan tube wasu manyan jami’an kula da lafiya a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.