Isa ga babban shafi
India

Majalisar Dokokin India ta tara miyagun mutane

Firaministan India Narendra Modi.
Firaministan India Narendra Modi. REUTERS/Altaf Hussain

Kotun Kolin India ta wajabta wa jam’iyyun siyasar kasar da su wallafa sunayen ‘yan takararsu da suka lashe kujeru a Majalisar Dokokin Kasar duk da cewa, sun aikata manyan laifuka da suka hada da kisa da fyade. Kotun ta kuma umarci jam’iyyun da su yi cikakken bayani kan yadda suka lashe zaben Majalisar Dokoki.

Talla

Kotun India ta ce, dole ne cikin gaggawa a kawo karshen yadda ake ci gaba da samun ‘yan siyasar da ke fitowa takara duk da cewa, manyan laifuka sun yi musu dabaibayi.

Yanzu haka, kotun ta bai wa jam’iyyun siyasar kasar sa’o’i 48 da su garzaya shafukunsu na intanet domin yin bayani game da wadannan ‘yan takara masu laifi.

A bara kadai, an samu kashi 43 na ‘yan Majalisar Dokokin Kasar da suka aikata manyan laifuka, alkaluman da suka zarce wadanda aka samu a shekarar 2014, inda a wancan lokacin aka samu kashi 34.

Wata Kungiyar Rajin Kare Dimokradiya ce ta ADR ta tattara alkaluman yayin da ake ci gaba da samun karuwar adadin sannu-a-hankali.

Daga cikin manyan laifukun da ake zargin ‘yan siyasar da aikatawa har da sata da cin zarafin jami’a da kisan kai har ma da fyade.

Kotun ta diga ayar tambaya kan dalilin da ke hana jam’iyyun siyasar tsayar da tsarkakakkun ‘yan takara da ba su da laifi a tattare da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.