Isa ga babban shafi
Lafiya-Amurka

Amurkawa 40 sun kamu da cutar Corona

Katafaren jirgin ruwan masu yawon shakatawa dake gabar ruwan Japan, da fasinjojinsa 335 suka kamu murar mashako ta Corona, ciki har da Amurkawa 40.
Katafaren jirgin ruwan masu yawon shakatawa dake gabar ruwan Japan, da fasinjojinsa 335 suka kamu murar mashako ta Corona, ciki har da Amurkawa 40. Kim Kyung-hoon/Reuters

Hukumomin kasar Amurka sun ce Yan kasar 40 dake cikin wani jirgin ruwan Japan da aka killace shi sun kamu da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 dake cigaba da hallaka jama’a.

Talla

Babban jami’in hukumar yaki da cutttuka masu yaduwa a kasar Anthony Fauci yace za’a kwantar da su a asibitin Japan domin kula da lafiyar su.

Shi dai wannan jirgi da aka killace shin a kwanaki 14 saboda gano wanda ya kamu da cutar na dauke da Yan kasashe da dama a cikin sa, kuma an tabbatar da cewar mutane 355 suka kamu da cutar.

Hukumomin Kasar China sun ce wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar yanzu haka sun zarce 1,600, yayin da suke cigaba da daukar matakan yaki da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.