Isa ga babban shafi
Irana-Corona

Coronavirus ta kashe Iraniyawa 2 a birnin Qom na kasar

Asibitin kula da masu dauke da cutar corona.
Asibitin kula da masu dauke da cutar corona. China Daily via REUTERS

Hukumomin kasar Iran sun ce wasu 'yan kasar guda biyu sun mutu sakamakon kamuwa da coronavirus ko kuma COVID-19 wadda ke cigada da salwantar da rayukan jama'a a kasar china.

Talla

Kafar talabijin din Iran ta ruwaito cewar mutanen biyu da suka mutu Iraniyawa ne mazauna birnin Qom wadanda suka zama mazauna Gabas ta Tsakiya na farko da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar, Kianoush Jahanpour ya ce sakamakon kamuwa da rashin lafiya da dattawan biyu suka yi, an musu gwajin da ya tabbara cewar coronavirus ce ta kama su, yayin da suka mutu lokacin da su ke tsaka da karbar kulawar likita.

Birnin Qom, cibiya ce ta addinin Islama wadda ke samun masu ziyara daga sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.