Isa ga babban shafi
corona - Japan

Coronavirus ta kashe mutane 2 dake jirgin ruwan yawo a Japan

Jirgin ruwan yawo bude ido na Diamond Princess
Jirgin ruwan yawo bude ido na Diamond Princess Reuters

Mutane biyu da suka kamu da cutar Coronovirus a jirgin ruwan yawon bude idon da aka killace a Japan sun mutu a safiyar Alhamis, yayin da aka tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu da suka kamu da cutar a kasar Iran.

Talla

Wadanda suka mutu a kasar ta Japan wato namiji daya da kuma mace daya, dukkaninsu tsofaffi ne da suka haura shekaru 80 a duniya a cewar kamfanin dillancin labaran kasar NHK.

A jimilce mutane 621 ne aka tabbatar da cewa sun harbu da kwayar cutar ta Coranavirus a wannan jirgi da ya isa kasar kimanin makonni biyu da suka gabata dauke da mutane 3,700 a cikinsa.

A can kuwa kuwa kasar Iran, ma’aikatar lafiya ta tabbatar da mutuwar mutane biyu bayan sun kamu da wannan cuta. Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ruwaito kakakin ma’aikatar lafiya Kianoush Jahanpour na cewa mutanen biyu sun mutu ne a garin Qom da ke kudancin birnin Tehran.

A can kuwa kasar China inda cutar ta samo asali, a yanzu alkaluman mamata sun tashi zuwa mutane 2,118 sakamako kamuwa da cutar, to sai dai duk da haka ana ganin cewa ana samun sauki ta fannin yaduwar ta a tsakanin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.