Isa ga babban shafi
China

Adadin wadanda annobar Corona ke halakawa a China ya ragu

Wasu jami'an lafiyar China a birnin Wuhan dake lardin Hubei, makyankyasar annobar murar mashako ta Coronavirus ko COVID-19.
Wasu jami'an lafiyar China a birnin Wuhan dake lardin Hubei, makyankyasar annobar murar mashako ta Coronavirus ko COVID-19. STR / AFP

Gwamnatin kasar China tace a jiya mutane 29 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, adadi mafi karanci tun daga watan jiya, yayin da cutar ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya da dama.

Talla

Alkaluman da hukumomin China suka bayar yau sun bayyana cewar adadin wadanda suka mutu a kasar ya kai 2,744, sakamakon samun sabbin masu dauke da cutar 433, yayin da aka samu mutuwar mutane 29.

Rahotanni sun ce an samu bazuwar cutar a kasashe da dama da suka hada da Girka da Georgia da Norway da Belgium da Sweden da Switzerland a Turai, sai kuma Brazil a Yankin Amurka ta kudu.

Sauran kasashen da cutar ta kutsa sun hada da Italia, inda aka killace garuruwa da dama, sai Faransa da Spain da Croatia da Austria da Findland da Jamus da Arewacin Macedonia da kuma Algeria.

Ita ma kasar Pakistan ta sanar da samun cutar kamar makotan China irin su Koriya ta kudu da Japan, sai kuma Iran.

Shugaba Donald Trump yace yana Nazari kan shirin hana Amurkawa zuwa kasashen Italia da Koriya ta kudu, yayin da ya nada mataimakin sa Mike Pence ya jagoranci shirin dakile cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.