Isa ga babban shafi
Pakistan

An kama likitocin da ke yaki da coronavirus

Likitoci 53 aka cafke saboda zanga-zangarsu ta neman a kare lafiyarsu a yayin yaki da coronavirus
Likitoci 53 aka cafke saboda zanga-zangarsu ta neman a kare lafiyarsu a yayin yaki da coronavirus REUTERS/Akhtar Soomro

'Yan sanda a Pakistan sun kama likitoci sama da 50 da suka gudanar da zanga-zangar lumana saboda bukatar samar musu da kayan aikin da za su kare lafiyarsu lokacin da suke kula da masu dauke da cutar COVID-19.

Talla

Rahotanni sun ce, an kama likitocin ne lokacin da suka yi gangami a gaban asibitin birnin Quetta kafin yin tattaki zuwa ofishin ministan da ke kula da birnin.

'Yan sanda sun yi amfani da kulake wajen tarwatsa likitocin kafin daga bisani suka kama 53 daga cikinsu, kamar yadda shugabansu Abdul Razzaq Cheema ya sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.