Isa ga babban shafi
India

India ta tsawaita dokar hana fita duk da korafin jama'a

Firaministan India Narendra Modi.
Firaministan India Narendra Modi. REUTERS/Altaf Hussain

Gwamnatin India ta tsawaita dokar tilasta wa mutane biliyan 1 da miliyan 300 zaman gida na dole har zuwa nan da ranar 3 ga watan Mayu mai zuwa domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Talla

Firaministan kasar, Nerandra Modi ya sanar da matakin duk da korafin da miliyoyin talakawan kasar ke yi na rashin tallafin da suke bukata, yayin da suka rasa ayyukan da suka dogara da su don samun abincin yau da kullum.

Mr. Modi ya bayyana cewa, matakin hana zirga-zirgar ya yi tasiri kan bangaren tattalin arzikin kasar, amma rayukan jama’a sun fi muhimmanci a cewarsa.

Kodayake Firaministan ya ce, nan da ranar 20 ga watan Aprilu, akwai yiwuwar fara sassauta dokar a wasu yankunan da ba a samu bullar cutar coronavirus ba, sannan gwamnati za ta fitar da sabbin sharuddan gudanar da ayyukan masana’atu da noma a gobe Laraba.

A kalla mutane 340 ne suka mutu sakamakon kamuwa da coronavirus a India, amma wasu kwararru a fannin kiwon lafiya na ganin cewa, adadin mamatan ya zarta haka nesa ba kusa ba, lura da cewa, kalilan daga cikin mutanen kasar aka yi wa gwajin cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta jinjina wa India kan matakin da ta dauka na tsawaita dokar zaman gida na dole a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.