Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta kashe mutane fiye da 70 a Saudiya

Saudiya ta dauki matakin hana zirga-zirga don hana yaduwar coronavirus
Saudiya ta dauki matakin hana zirga-zirga don hana yaduwar coronavirus Reuters

Gwamnatin Saudiya ta sanar da samun karin mutane 8 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, abin da ya kawo adadin mamatanta a sanadiyar wannan cuta zuwa 73.

Talla

Mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiyar Kasar, Dr. Muhammed Al-Abdel Ali ya ce, ya zuwa yanzu mutane dubu 5 da 369 suka kamu da cutar a Saudiya, inda ake da 114 a birnin Riyadh, 111 a Makkah, sai kuma 69 a Dammam,  yayin da aka samu 50 a Madinah, sai kuma 46 a  birninJeddah.

Dr. Ali ya ce, akwai mutane 16 da suka kamu da cutar a Hufof, 10 a Buraidah, 7 a Dharan, 4 a Tabuk, kana guda-guda a Hail da Kharj da Al-Khobar da Samtah da Bisha da Abha da Al-Baha da kuma Taif.

A makon jiya ne, gwamnatin Saudiya ta yi gargadi kan barazanar samun masu dauke da cutar coronavirus har mutun dubu 200 nan da 'yan makwanni masu zuwa a kasar. 

Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin kasar ta  tsawaita dokar hana fita a biranen Makkah da Madina da wasu manyan garuruwa da suka hada da birnin Riyadh har tsawon sa'o'i 24.

Ministan Lafiyar Saudiya, Tawfiq al-Rabiah ya ce, binciken masana a ciki da wajen kasar ya nuna cewar, daga mutane sama da dubu 2 da cutar ta harba yanzu haka a kasar, adadin na iya tashi zuwa dubu 200 saboda yadda cutar ke yaduwa.

Wannan annobar ce, ta sanya mahukuntan Saudiya suka bukaci kasashen Musulmi na duniya da su jinkirta shirye-shiryensu na zuwa aikin hajjin bana saboda yaduwar coronavirus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.