Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Rashin ganin shugaba Kim a bainar jama'a ya janyo ce-ce-kuce

Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa.
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa. Alexander SAFRONOV / Press Service of Administration of Primorsk

Hotunan tauraron dan adam sun nuna wani jirgin kasa mai kama da wanda Kim Jong-un shugaban Koriya ta Arewa ke amfani da shi, a gabashin kasar ta Koriya.

Talla

Hotunan wadanda aka dauka tsakanin ranar 21 da 23 ga wannan wata na Afrilu, sun nuna jirgin kasan a wata tasha ta musamman da ga al’ada aka saba ware wa iyalan shugaba Jong-un.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke

nuna cewa shugaban na fama da rashin lafiyar da ta shafi zuciyarsa, har wasu ma ke zargi da yada jita-jitar shugaban na Korea ya mutu, amma aka boye labarin.

Tun ranar 15 ga wannan wata ne aka fara nuna shakku a game da lafiyar shugaban, sakamakon rashin bayyanarsa a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar kakansa Kim Il Sung wanda ya kafa tsarin Kwaminisanci kda kasar ke tafiya a kansa.

Daily NK, shafin yada labarai na ‘yan asalin Koriya ta Arewa da ke adawa da salon mulkin kasar, ya ruwaito cewa shugaban na fama da matsalar bugun jini, wadda tuni ta shafi wani bangare na jikinsa, kuma yana ci gaba da jinya a daya daga cikin gidajensa da ke lardin Pyongan na arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.