Isa ga babban shafi

Dakarun Turkiya sun kaddamar da farmaki a Syria

Talla

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan, yace dakarun kasar sun kaddamar da sabon farmaki kan mayakan Kurdawa, da kuma ragowar mayakan IS, masu iko da wasu yankuna a arewacin Syria. An dai shafe tsawon lokaci Turkiya na shirin kaddamar da farmakin kan mayakan Kurdawan na kungiyar YPG masu alaka da jam’iyyarsu ta PKK da Turkiyan ta haramta, sakamakon yakin neman ballewa daga kasar da ta shiga tun daga shekarar 1984.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.