Isa ga babban shafi
Chuchin Katolika

Limaman Chuchin Katolika Sun Nemi Gafara

Reuters

Limaman Chuchin Katolika sun nemi gafara. Manyan limaman Chuchin Darikar Katolika dake Ingila da Whales masu magoya baya samada milliyan 5 ayau sun nemi gafara saboda abin kunyan nan da ake dorawa wasunsu na lalata da yara.Sun fadi cikin wata sanarwa ayau cewa babu shakka wannan abin kunya ne ga Chochin.Sanarwan na kunshe ne da sa hannun Acibishop na Westminister Vincent Nichols amadadin sauran manyan Limaman, inda tayi bayanin  cewa babu wani abin kunya da takaici daya wuce wannan abu.Sanarwan na cewa bama kawai abin kunya ne ga mabiya darikar ba, katon laifi ne, har ga Allah mahalicci.Sukace wasu yan kalilan ake tuhuma da wannan laifi amma kuma wannan abu ya bata sunan magoya bayan Chuchin Katolika dake fadin duniya.Wannan sanarwa dai na zuwa ne adaidai wani lokaci da Paparoma Benedict XV1 ke karban takardan amincewa da ajiye aiki na Bishop na Irish James Moriarty da ake zargi da yin rufa rufa da mafanar lalata da yara kanana da akeyiwa wasu limaman chuchin na Katolika.James Moriarty, acikin takardan ajiye aikin ya nemi gafara inda yace da bai yarda ba yaki bayyana lamarin lalata da yaran akan lokaci.  

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.