Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Hollande ya kai ziyara kasar Mali domin fara shirin mika kasar ga dakarun Afrika

Shugaban kasar Faransa, François Hollande (Hagu) tare da takwaransa na kasar Mali, Dioncounda Traoré a lokacin da ya kai ziayar kasar Mali.
Shugaban kasar Faransa, François Hollande (Hagu) tare da takwaransa na kasar Mali, Dioncounda Traoré a lokacin da ya kai ziayar kasar Mali. AFP / FRED DUFOUR

Dubban mutane ne suka tarbi Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a yau Asabar yayin da ya kai ziyara kasar domin share fagen mika kasar ga dakarun Afrika, bayan kasar ta Faransa ta jagoranci fatattakar ‘Yan tawayen da suka mamaye Arewacin kasar. Ziyarar ta biyo bayan karbe garin kidal daga hanun ‘Yan tawayen wadanda suka mamaye garin wanda shine gari na karshe dake hanunsu da suka karbe bayan wani juyin mulkin da soji suka yi a kasar a bara.  

Talla

An tarbi Hollande ne a dandalin Central Sqaure dake garin Timbukutu wanda shima da yake hanun ‘Yan tawayen a farkon makon da ya gabata, inda rahotanni suka ruwaito cewa anga dubban mutane na ta rera waka suna rawa nuna farin cikinsu.

“Mun riga mun gudanar da ayyuka da dama, amma har yanzu da sauran aiki, zai dauki makwannin da yawa, amma burinmu shine mu mika ikon kasar ga dakarun Afrika domin bamu da niyyar mu yi ta zama anan.” Hollande ya gayawa taron jama’ar kasar.

A daya bangaren, Shugaban rikon kwaryar kasar, Diancounda Traore, wanda ya rike hanu da Hollande a lokacin ziyarar, ya mika godiyarsa ga takwaransa na taimakon dakaru da aka ba kasar ta Mali.

Akalla dakarun Nahiyar Afrika kusan 8,000 ake sa ran za a mikawa ikon kasar ta Mali, yayin da sauran kasashen nahiyar ke ta aikewa da nasu dakarun.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.