Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

An tabka hasara mai dimbin yawa saboda canjin yanayi

Garin Tacloban na kasar Philppines da Guguwr Haiyan  ta share a ranar 9 novembre 2013.
Garin Tacloban na kasar Philppines da Guguwr Haiyan ta share a ranar 9 novembre 2013. Reuters

Bankin Duniya yace adadin kudaden da ake hasara sakamakon annobar da canjin yanayi ke haifarwa sun kai Dalar Amurka Biliyan 200, inda suka rubanya adadin hasarar da ake yi sau 4 na tsawon shekaru 30 da suka gabata.  

Talla

Bankin na Duniya yace irin yadda yanayi ke canzawa haka kudaden da ake hasara da barnar da sauyin yanayin ke haifarwa ke ci gaba karuwa.

Babban Bankin ya fadi haka ne a taron canjin yanayi a birnin Wawsaw, inda bankin yace an yi hasarar kudi Dala Tiriliyan 4 a shekaru 30 da suka gabata sakamakon tsawa da guguwa mai tafe da iska da kuma ambaliyar ruwa. Al’amarin da kuma ya janyo hasarar rayukan mutane sama da Miliyan 2 da rabi.

Munmunar guguwar Haiyan da ta shafi kasar Phillipines, ta daga hankalin duniya, inda masana suka ce ita ce guguwa mafi muni da aka samu a duniya.

Rahoton na Bankin Duniya yace ire iren bala’in da ake samu sakamakon canjin yanayi, babbar matsala ce, da ke gurgunta tattalin arzikin duniya.

A Nahiyar Afrika, Rahoton na Bankin Duniya yace kusan sama da kashi 13 na Miliyoyan mutanen nahiyar ne suka shiga matsalar karancin abinci saboda fari.

Bankin Duniya yace, akwai bukatar kasashe su dauki matakan gaggawa tare shirin ko-ta-kwana domin kaucewa wata annoba da canjin yanayi zai haifar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.