Isa ga babban shafi
Honduras

An tabbatar da Hernandez a matsayin shugaban Honduras

Juan Hernandez da aka bayyana a matsayin zababben shugaban kasar Honduras
Juan Hernandez da aka bayyana a matsayin zababben shugaban kasar Honduras REUTERS/Jorge Cabrera

Kotun da ke kula batutuwan da suka shafi zabuka a kasar Hunduras, ta tabbatar da sunan Orlando Hermandez a matsayin zababben shugaban kasar, bayan al’ummar kasar sun jefa masa kuri’a a ranar 24 ga watan Nuwambar da ya wuce. Kotun ta ce sabon shugaban zai soma wa’adin mulkinsa ne daga ranar 27 ga watan Janairun badi zuwa 27 ga watan Janairun 2018, abinda ke ta tabbatar da cewa kotun ta yi watsi da bukatar soke sakamakon wannan zabe da tsohon shugaban kasar Manuel Zelaya ya gabatar a gabanta.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.