Isa ga babban shafi
Birtaniya-Iraq

Birtaniya zata yi jigilar makamai zuwa Iraqi

'Yan Yazidi suna zanga-zangar adawa da Mayakan IS da suka kore su daga gidajensu
'Yan Yazidi suna zanga-zangar adawa da Mayakan IS da suka kore su daga gidajensu REUTERS/Wolfgang Rattay

Kasar Birtaniya tace za ta yi jigilar makamai zuwa ga Kurdawan Iraqi wadanda ke yaki da mayakan ISIS a Arewacin kasar. Ofishin Firaminsitan kasar David Cameron yace Birtaniya za ta karbi makamai daga kasashen da ke shirin bayar da gudumawa don kai wa Kurdawan. Sai dai ya zuwa yanzu ba’a bayyana kasashen da suka yi tayin bada makaman ba.

Talla

Tuni dai Birtaniya tace ba zata dauki matakin da Amurka ta dauka ban a kai farmaki ta jiragen sama a yankunan Iraqi amma zata bayar da gudunmuwa a bangaren jin kai.

Rahotanni sun ce Mayakan IS sun karbe ikon wasu kauyuka a arewacin Syria kusa da Aleppo, kamar yadda kungiyar kare hakkin bil’adama da ke sa ido a rikicin Syria ta tabbatar.

Mayakan IS suna gwagwarmayar tabbatar da sabuwar daular Islama da suka ayyana bayan sun karbe wasu yankunan Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.