Isa ga babban shafi
Gaza

An cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Falasdinawa da suka bazama saman tituna suna murna bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa a Gaza
Falasdinawa da suka bazama saman tituna suna murna bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa a Gaza REUTERS/Suhaib Salem

An share tsawon daren jiya ana gudanar da shagulgula a zirin Gaza, sakamakon kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, bayan share tsawon kwanaki 50 ana fafatawa tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Yarjejeniyar wadda ta soma aiki tun karfe 4 na marecen jiya, da farko ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta domin kawo karshen wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 2,143 da kuma wasu Yahudawan su 69.

Wasu daga cikin manyan batutuwan da ke cikinta sun hada da gaggauta buda kofofi domin shigar da kayayyakin jinkai da na gine-gine ga mazauna yankin Gaza, kamar dai yadda ma’aikatar harkokin wajen Masar da ke shiga tsakanin bangarorin biyu ta sanar.

A bangaren Hamas dai an bayyana yarjejeniyar da cewa ta dindindin ce, yayin da wani babban jami’an gwamnatin Isra’ila ke tabbatar da cewa lalle yarjejeniyar ba ta da wani wa’adi da za a kawo karshen aiki da ita.

Mai Magana da yawun Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry Jen Psaki, ta ce Amurka na goyon bayan tsagaita wutar.

Gwamnatin Kasar Qatar da ke nuna goyon baya ga Mayakan Hamas ta yi alkawalin bayar tallafi domin gina sabuwar Gaza da Isra’ila ta twarwatsa a tsawon makwanni bakawai tana kai farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.