Isa ga babban shafi
Honduras

Ana zanga zangar adawa da shugaban kasar Honduras

zwasu masu zanga zanga a kasar Honduras
zwasu masu zanga zanga a kasar Honduras REUTERS/Jorge Cabrera

Dubun dubatar ‘yan kasar Honduras sun yi zanga zangar neman a gudanar da bincike kan shugaban kasar, Juan Orlando Hernandezm da ake zargi da hannu a wata badakalar cin hanci. Tawaggar masu zanga zangar sun gamu da juna a kusa da fadar shugaban, inda wasu masu yajin kin cin abinci suka yi tantunan da suke kwana, don isar da sakon nasu. 

Talla

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun dauki fitilu yayinda wasu kuma ke rike da takardun dake nuna shugaban sanye da kayan ‘yan fursuna.
Tun cikin watan Mayu ake zanga zangar adawa da shugaba Hernandez, da ake zargi da amfani da kudaden gwamnati, a yakin neman zabensa na shekarar 2013.
Dama shugaban ya amsa cewa jam’iyyarsa ta Conservative ta karbi makudan kudade, daga wani asusun tallafawa masu karamin karfi.
‘Yan adawan kasar ma sunce an wawashe wasu kudaden daga asusun kula da lafiyan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.