Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta bukaci Turai ta magance kwararar 'Yan gudun hijira

Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon.
Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki- Moon ya bukaci kasashen Turai da su kara kaimi wajan tinkarar matsalar kwararar ‘Yan gudun hijira.

Talla

Mr. Ban ya bayyana haka a jawabinsa na sharen fage a taron Majalisar da aka bude a ranar litinin a birnin New York na Kasar Amurka.

Mr. Ban ya shaidawa taron Majalisar Dinkin duniya mai kunshe da kasashe 193 cewa akwai bukatar nahiyar Turai ta kara kaimi wajan tinkararr matsalar kwararar ‘Yan gudun hijirar da aka bayyana a matasayin mafi kamari tun bayan yakin duniya na biyu.

Sakaten ya kara da cewa, bai kamata a ci gaba da sanya shingaye ba a kan iyakokin kasashen Turai ba domin hana Yan gudun hijirar kutsawa cikin nahiyar, yayin da ya ja hankulan mahukunta, inda ya ce ya kamata a duba abin da ke tirtsasawa Yan gudun hijrarar kauracewa kasashensu na asali.

Sama da mutane miliyan hudu ne suka kauracewa gidajensu a cikin shekaru hudu sakamakon yakin da ake fama da shi a Kasar Syria, lamarin da yasa dubban jama’a neman mafaka a Turai.

Ana sa ran Sakateren na Majalisar Dinkin Duniyar, zai jagoranci wani taro dabam a ranar laraba domin tattauna wa kan matsalar kwararar yan gudun hijirar, inda ake fatar cimma matsaya ta yadda sauran kasashen duniya zasu amince da tinkarar matsalar yayin da kungiyar tarayyara Turai ke nata kokarin shawo kan matsalar.

a makon da ya gabata ne Tarayyar Turai ta amince ta bada dalar Amurka biliyan guda a matsayin tallafi a aikin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na agazawa 'Yan gudun hijrar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.