Isa ga babban shafi
Paris

Masana kimiyar yanayi sun yi na’am da yarjejeniyar da aka cim ma

Wakilan kasashe 195 sun amince da yarjejeniyar rage dumamar yanayi a taron da aka gudanar a Paris
Wakilan kasashe 195 sun amince da yarjejeniyar rage dumamar yanayi a taron da aka gudanar a Paris REUTERS/Mal Langsdon

Masana kimiyar yanayi sun yi na’am da yarjejeniyar da aka cim ma ta rage dumamar yanayi a Paris, amma sun ce har yanzu akwai gibi, ga bayanin tsarin yadda kasashe zasu rage gurbataccen iska da ke haifar da matsalar.

Talla

A ranar Asabar ne kasashe 195 suka amince da yarjejeniyar da ta kunshi rage dumamar yanayin zuwa kasa da biyu na ma’aunin yanayi.

Masanan na ganin akwai bukatar a rage fitar da dattin hayaki da masana’antu ke fitarwa da kusan kashi 70 zuwa 90 daga yanzu zuwa shekaru 50.

Yarjejeniyar da aka amince a Paris ta shiga cikin kundin tarihi a duniya inda ake ganin matsalar dumamar yanayi babbar matsala ce ga rayuwar bil’adama.

China mai yawan fitar da gurbsataccen iska ta yi na’am da yarjejeniyar .

Shugaban Amurka Barack Obama yace wannan dama ce ta ceto duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.