Isa ga babban shafi
Ecuador

Mutane 233 ne suka mutu a girgiza Kasa a Ecuador

Girgizar kasar Ecuador
Girgizar kasar Ecuador Reuters/路透社

Mutane akalla 233 ne aka tabbatar da mutuwarsu a kasar Ecuador kamar yadda sanarwar shugaban kasar Rafael Correa ke cewa, shugaban ya yi bayani akan matakin gwamanti na  kai doki ga al'ummar yankin da girgizar ta shafa  

Talla

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 a ma'aunin rishta ta kasance mafi muni a tsawon shekaru,yanzu baya ga 233 da aka tabbatar da mutuwarsu akwai wasu kusan 600 da suka sami munanan rauni, Mataimakin shugaban kasar Jorge Glas ya ce yawan mamata zai karu saboda ana cigaba da aikin ceto

An bayyana cewa anji rugugin girgizar kasar a koina ciki da wajen kasar, tuni dai shugaban kasar dake Ziyara a kasar Italiya ya katse wannan ziyara tare da rugawa yankin Guayaquil inda al'amarin ya auku, an dai bayyana dokar ta baci a yankuna shida dake kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.